Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko kadan al'ummar Sinawa ba za su yarda da zaluncin da ake son yi wa kasarsu ba bisa annobar Covid-19
2020-05-06 21:08:26        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Madam Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, gangamin nuna kin jinin mulkin danniya da dalibai suka gudanar a kasar Sin na ran 4 ga watan Mayun 1919, ba wai gangami na talakawa ba. Idan har yanzu Amurka na son dora laifin annobar Covid-19 a kan kasar Sin, da kuma yi wa kasar zalunci, lalle al'ummar kasar biliyan 1.4 za su nuna kin amincewa.

A ranar 4 ga watan nan ne, mataimakin mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa Matthew Pottinger, ya bayyana cewa, wadanda suka gaji manufar gangamin nuna kin jinin mulkin danniya da dalibai suka gudanar a kasar Sin, na ran 4 ga watan Mayun 1919, al'ummar kasar Sin dake sane da cewa, su ma 'yan kasar ne.

A game da furucin, Madam Hua Chunying ta bayyana a taron manema labarai cewa, ainihin manufar gangamin shi ne kishin kasa. Game da annobar Covid-19, al'ummar Sin sun hada karfi da karfe, har ma sun samu gaggaruman nasarori wajen shawo kan cutar, lamarin da ya bayyana ainihin waccan manufa a wannan zamanin da muke ciki. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China