Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Duk wani yunkurin bata sunan kasar Sin zai bi ruwa
2020-04-14 20:09:11        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, kasar Amurka ta yi amfani da wani batu don shiga tsakani kan dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma lalata dadadden zumuncin dake tsakanin bangarorin biyu, irin wannan mataki da ta dauka ba zai yi nasara ba, kuma rashin da'a ne.

Kakakin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Talata a nan birnin Beijing.

Bayanai na nuna cewa, jiya Litinin mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka mai kula da harkokin Afirka Tibor P. Nagy ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, bidiyon da aka dauka kan abin da ya faru a birnin Guangzhou abin mamaki ne, a nasa bangaren kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Morgan Ortagus ya sake wallafa kalaman, tare da bayyana cewa, wannan kyamar baki abin kunya ne.

Game da tambayar da aka yi masa kan batun, kakakin ya ce, "Ina so in jaddada cewa, akwai zumunci mai karfi a tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka, kuma babu wanda zai lalata shi. Bayan bullar cutar COVID-19, bangarorin biyu su kara hada kansu don tinkarar mawuyacin halin da ake ciki. Duk wani mataki na bata sunan kasar Sin, da yunkuri na neman raba kai da takala ba za su yi nasara ba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China