![]() |
|
2020-05-03 17:31:07 cri |
Ya ce, a yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19, kasar Sin ta baiwa Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka babbar gudummawa ta fannonin kayayyakin kiwon lafiya da ma bayanai da fasahohin dakile cutar. Ya kara da cewa, "Ofisoshin jakadancin kasar Sin da kamfanonin kasar da ma sassa masu zaman kansu na kasar duka suna kokarin daukar matakai, al'amarin da ya cancanci yabo.
Ambassada ya ce, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a shekarar 1971, kasashen biyu suna martaba juna da cin moriyr juna da kuma hadin gwiwa da juna. Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar hadin gwiwa ga Nijeriya wajen aiwatar da ayyukan gina hanyoyin dogo da filayen jiragen sama da hanyoyiin mota da sauransu, kuma kamfanonin kasar Sin ma na bunkasa yadda ya kamata a Nijeriya. Al'ummar Nijeriya ma suna rungumar kayayyaki kirar kasar Sin. Ya ce, a kokarin da ake na shawo kan cutar, Nijeriya za ta nuna tsayayyen goyon baya ga kasar Sin, yana kuma jan hankalin al'ummar Nijeriya dake kasar Sin da su bada hadin kai ga hukumomin kasar wajen aiwatar da matakan dakile cutar.(Lubabatu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China