Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya ya karu zuwa 407
2020-04-16 19:57:30        cri
Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya karu zuwa 407, bayan da aka samu rahoton sabbin mutane 34 da suka kamu da cutar.

A bayanan da ta fitar a daren jiya Laraba, cibiyar ta ce ya zuwa yanzu, cutar ta halaka mutane 12 kana an sallami mutane 128 bayan da aka tabbatar sun warke daga cutar a kasar da ke yammacin Afirka.

Mutane na baya-bayan da suka kamu da cutar, an same su ne a jihohin Lagos,da Kano, da Katsina da Delta, da kuma jihar Niger.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China