Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sanya abin rufe baki da hanci a yankin babban birnin kasar Ghana ya zama tilas
2020-04-24 10:10:16        cri
Rahotanni daga Accra, babban birnin kasar Ghana na cewa, majalisar tsaron yankin, ta umarci jama'a da su rika sanya abin rufe baki da hanci, a wani mataki na kara yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Wata sanarwa da majalisar tsaron ta fitar jiya Alhamis ta bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne don karfafa tasirin sauran matakan da gwamnati ta dauka na hana yaduwar annobar a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, majalisar tsare-tsaren, za ta fito da managartan matakan ilmantar da jama'a da rage cunkoso a wasu kasuwanni dake yankin.

Baya ga dakatar da wasu ranakun da ake cin kasuwa na musamman a wasu cibiyoyin kasuwanni, sanarwar ta ce " duk wanda bai sanya abin rufe baki da hanci ba, to ba zai shiga ba". Za kuma a sanya alama a muhimman wurare a tashoshin mota, da wuraren taruwar jama'a, da shagunan zamani, da bankuna da sauran wuraren taruwar jama'a. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China