Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban editan mujallar The Lancet: Dakatar da samarwa WHO kudi da Amurka ta yi tamkar laifi ne ga dukkan dan Adam
2020-04-16 11:04:27        cri

Babban editan mujallar "The Lancet" Richard Horton, ya bayyana a jiya cewa, matakin gwamnatin kasar Amurka na dakatar da samarwa hukumar lafiya ta duniya WHO kudi, kamar wani laifi ne ga dukkan dan Adam.

Editan ya kuma yi kira ga duk 'yan kimiyya, da likitoci, da sauran al'umma da su nuna kin amincewa da wannan mataki na sabawa hadin kan duniya. Daga bisani sai Mr. Horton ya tunatar da shugaban cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa ta kasar Amurka Anthony Fauci ta kafar internet cewa, zargin shugaban kasar Amurka kan hukumar WHO ba shi da tushe, ya kamata a gyara wannan kuskure, a bi gaskiya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China