Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afrika 39 za su samu tallafin GPE don yaki da COVID-19
2020-04-09 10:14:51        cri

Shirin hadin gwiwar bunkasa ilmi na kasa da kasa wato Global Partnership for Education ko kuma GPE a takaice, ya amince zai bayar da tallafin dala miliyan 250 ga kasashen Afrika 39 da wasu kasashe masu tasowa 28 domin yaki da annobar COVID-19.

An amince da matakin ne a yayin taron hukumar daraktocin GPE da suka gudanar ta kafar bidiyo a ranar Talata, shirin zai taimakawa kasashe masu tasowa wajen rage tasirin da annobar COVID-19 za ta haifar ga tsarin ilmi na gajere da kuma dogon zango.

Shirin na GPE ya kara da cewa, kudaden za su taimakawa ilmin yara sama da miliyan 355, kuma zai fi bayar da fifiko ne ga ilmin 'yaya mata da yara marasa galihu, wadanda rufe makarantun da aka yi zai yiwa mummunan tasiri, shirin zai ba su damar ci gaba da karatunsu.

Daga cikin kasashen duniya 67 da za su ci gajiyar shirin na GPE, tuni kasashe 63 sun riga sun ba da umarnin rufe makarantunsu sakamakon barkewar annobar ta COVID-19.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China