![]() |
|
2020-04-08 12:46:05 cri |
Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, masanan kasar Sin, da tawagogin likitoci masu ba da taimako ga kasashen Afirka, da kamfanonin kasar Sin da dama suna yin hadin gwiwa da kasashen Afirka ta hanyoyi daban daban domin yaki da annobar, lamarin da ya nuna dunkulewar kasashen Sin da Afirka.
Yanzu, akwai likitocin kasar Sin kimanin dubu 1 dake aiki a kasashen Afirka, inda suke ba da goyon baya ga kasashen wajen kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ya zuwa yanzu, sun riga sun gudanar da ayyukan horaswa kan ilmin kiwon lafiya sama da 250, inda suka ba da horo ga mutane sama da dubu 10.
Haka kuma, kasar Sin ta kafa tawagogin masana masu ba da shawara, domin yin mu'amala da likitocin kasashen Afirka 54 ta kafar bidiyo.
Ban da haka kuma, a ranar 6 ga wata, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar ga kasashen Afirka guda 18 sun sauka a kasar Ghana. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China