Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsoffi 7 da shekarunsu na haihuwa sun zarce 100 sun warke a asibiti
2020-04-12 19:16:17        cri

Wata jami'ar kwamitin lafiyar kasar Sin Jiao Yahui a jiya Asabar ta ce, wasu tsoffi 8 da shekarunsu na haihuwa ya zarce 100 wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Wuhan na kasar, 7 daga daga cikin su sun warke, kuma an sallame su daga asibiti, daga cikin tsoffin akwai wanda shekarunsa ya kai 108.

Jami'ar ta ce, yawan mutanen da suka kamu da cutar da suka warke bayan samun jinya ya kai kashi 94%, ciki kuwa wadanda shekarunsu na haihuwa ya kai 80 yawansu da suka warke daga cutar ya kai kusan kashi 70%. Wadannan nasarori da kyar ake iya cimmawa. A cikin wadanda suka kamu da cutar a birnin, yawan shekarunsu na haihuwa sun wuce 80 ya kai 3000 da wani abu, kashi 40 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

An ce, a cikin wadannan tsofaffi, sama da kashi 90% sun kamu da wasu cututtuka na tushe, wasu dake cikin mawuyacin hali suna samun kulawa a asibiti har tsawon kwanaki kusan 60. Bisa tsarin bada jinya ga masu kamuwa da cutar a Wuhan, an dauki matakai daban daban bisa halin da masu kamuwa da cutar suke ciki. Wato wadanda shekarunsu na haihuwa suke kasa da 65 kuma ba su kamu da sauran cututtukan na tushe ba, za su samu jinya a asibitocin na wucin gadi, wadanda shekarun haihuwarsu suka wuce 65, suka kamu da cutukan daga tushe, za su kwanta a asibitoci masu inganci.

Jami'ar ta kara da cewa, "akwai wahala wajen yin jinyar tsofaffi masu kamuwa da cutar, kuma ana kashe kudi masu yawa da amfini da jerin kayayyakin lafiya a kansu. Amma a yayin da ake jinyarsu, ba a nuna musu banbanci sakamakon ko su masu arziki ne ko matalauta, da yawan shekarun haihuwa da kuma jinsi."

Ko da yaushe, kasar Sin tana mayar da tsaron rayuwar jama'arta da lafiyarsu a gaban kome a yayin da take kokarin yakar cutar. Ya zuwa ranar 10 ga wata, adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 50008 a birnin Wuhan, wadanda suka warke kuma aka sallama daga asibiti sun kai 47112, wadanda har yanzu ke cikin mawuyacin hali a asibiti sun ragu zuwa 94. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China