Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bill Gates: kyawawan fasahohin kasar Sin za su kawo manyan sauye-sauye kan yaki da annobar COVID-19 a duniya
2020-04-10 20:53:39        cri

Jiya ne, Bai Yansong, wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya zanta da Bill Gates, shugaban asusun Bill Gates na kasar Amurka.

Dangane da sake bude birnin Wuhan da mahukuntan kasar Sin suka yi a ranar 8 ga wata, Bill Gates ya ce, ya yi imani da cewa, a lokacin da aka hana shigi da fici daga Wuhan, kowa ya sha wahala, ya kamata a taya su murna bayan sake bude birnin. A matsayinta na kasar da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta fara bulla, kasar Sin ta fuskanci babban kalubale. Amma yanzu tana taimakawa sauran kasashe. Kusan dukkan ma'aikata sun koma bakin aiki, wadanda suke samar da wasu muhimman kayayyakin yaki da annobar, hakan zai taimaka wajen kawo manyan sauye-sauye kan yaki da annobar a duniya.

Haka zalika, Bill Gates ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa. A ganinsa, muddin ba a hada kai ba, to ba za a iya daidaita mummunar yaduwar annoba a nan gaba ba. Idan an taimaka wa dukkan kasashe suka kawar da annobar, hakan zai yi babban tasiri kan yadda za a daidaita sauyin yanayi.

Bill Gates ya yi nuni da cewa, yaduwar annobar ta COVID-19 ta shaida cewa, kowa da kowa na dogaro da juna, haka lamarin yake tsakanin kasa da kasa. Akwai bukatar samar da kwarewa, allurar rigakafi da maganin da ya dace, wajen hana yaduwar annobar. Ya zama tilas a yi la'akari da dukkan kasashen duniya, ba wata kasa daya ita kawai ba. A yi kokarin rage farashin allurar rigakafi mafi kankanta. A kuma tattara kudade wajen sayen allurar, a kokarin ganin an yi wa kowa da kowa a duniya allurar.

Har ila yau, Bill Gates ya yi hasashen cewa, a nan gaba kasar Sin za ta iya kara taka rawa mai yakini wajen yin hadin gwiwa da kasashen duniya wajen dakile yaduwar annobar. Ya ce, asusunsa, da kasar Sin da sauran kasashe za su kara hada kai domin ba da taimakon yaki da annobar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China