Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Birtaniya da Jamus: Mai yiyuwa ne COVID-19 ta fito daga kasar Amurka da Australiya a bara
2020-04-11 15:51:18        cri

Bincike ya nuna cewa, kwayar cutar COVID-19 na sauyawa yayin da take yaduwa, lamarin da ya ba masana kimiyya damar bibiyar asalinta da kuma yadda yanayinta zai zama a nan gaba.

An yi ammana cewa, kwayar cutar, wadda asalinta ke da alaka da Jemagu da dabbobin Pangolin, ita ce masana ke wa lakabi da nau'in "Type A". Daga wajen kasar Sin, an fi samun irin wannan nau'i "Type A" ne a Amurka da Australia. Nau'in na 'Type A' ne ya sauya zuwa nau'in 'Type B', wanda kuma ya sauya zuwa 'Type C', wanda kuma irinsa aka fi samu a Turai.

Masana kimiyyar sun lura cewa, kusan ba a samun nau'in 'Type B' sai a gabashin Asia, wanda ya kai su ga son gano ko mutanen dake wajen yankin suna da wata kariya daga irin nau'in.

Za a iya amfani da nazarin da masana kimiyyar daga jami'ar Cambridge, da jami'ar Kiel da Cibiyar nazarin kwayoyin halitta ta Jamus da cibiyar kiwon lafiya ta Lakeside dake Birtaniya suka yi wajen tsara taswirar yaduwar cutar a fadin duniya.

An kuma wallafa sakamakon binciken cikin rahoton cibiyar nazarin kimiyya ta Amurka.

Daga bisani, masanan sun yi ittifakin cewa, kwayar cutar ta fara kama dan adam ne tsakanin tsakiyar watan Satumba da farko watan Disamban 2019. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China