Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yi gargadin yaduwar COVID-19 a karkarar Afrika saboda raunin tsarin kiwon lafiya
2020-04-10 11:47:25        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi gargadin yiwuwar barkewar annobar COVID-19 cikin sauri a yankunan karkarar Afrika saboda barazanar da ake fuskanta na rashin ingancin asibitoci da kayayyakin aikin lafiya a yankunan.

Matshidiso Moeti, darakatan hukumar WHO a shiyyar Afrika, ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta daukar matakan dakile bazuwar annobar COVID-19 daga manyan birane zuwa yankunan karkarar nahiyar domin kaucewa mummmunan tasirin da hakan zai haifar ga tsarin kula da lafiyar al'umma.

Alkaluman da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC ta fitar na baya bayan nan sun nuna cewa, sama da mutane 10,000 ne suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar, yayin da yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar annobar ya zarce 500 a Afrika.

Hukumar lafiyar ta duniya ta ayyana cewa, kasashen Afrika za su iya samun nasarar dakile annobar ta COVID-19 idan har suka zuba kudade wajen samar da karin cibiyoyin kula da marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani da samar da kayayyakin ba da kariya ga jami'an kiwon lafiya da sauran jama'a.

Hukumar ta yabawa kasashen Ghana, Kenya da Najeriya, saboda suka kafa dakunan gwaje gwaje masu yawa da kara fadada cibiyoyin gwajin cutar a kasashensu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China