2020-04-06 17:21:51 cri |
Rahoton rana-rana da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gabatar a daren jiya Lahadi 5 ga watan nan, ya yi nuni da cewa, yanzu haka matsin lambar da kasar Sin take fuskanta wajen kandagarki, da dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ya dan yi sauki. Kasar ta kuma samu managartan dabaru masu muhimmanci, na yaki da wannan munanar annoba.
Rahoton ya ruwaito kalaman Gauden Galea, wakilin WHO da ke nan kasar Sin, wanda ke cewa kasar Sin ta samu muhimman fasahohin kandagarki, da na dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, musamman ma kasancewar ta dauki wasu matakai, bisa hakikanin halin da take ciki, ta kuma aiwatar da wasu matakan kiwon lafiyar al'umma a wurare daban daban, bisa mabambantan halin da wadannan wurare suke ciki, lamarin da ya taimaka mata wajen hana yaduwar annobar yadda ya kamata.
Babban jami'in na WHO ya kara da cewa, al'ummar kasar Sin sun yi namijin kokarinsu, wajen dakatar da yaduwar annobar ta COVID-19 a kasarsu, da ma dukkanin duniya baki daya, ta hanyoyin tabbatar da nisantar juna tsakanin jama'a zuwa tazarar mita 1 da rabi, yayin da ake mu'amala da juna, da killace mutanen da suka taba yin mu'amala da masu dauke da cutar, da inganta matakin wanke hannu, da sauran matakan kiwon lafiyar mutane, matakan da suka haifar da sakamako mai kyau.
Gauden Galea ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya su hada kansu, su aiwatar da dabarun kandagarki, da dakile yaduwar annobar, da kuma bayanan yaduwar annobar, su yi koyi da juna, su kuma dauki matakai masu nasaba da yakar annobar a kan lokaci.
Adadin kididdigar da hukumar WHO ta gabatar ya nuna cewa, ya zuwa karfe 6 na yammacin jiya Lahadi bisa agogon tsakiyar Turai, mutane 1,136,851 sun kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya, yayin da mutum 62,955 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China