Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tabbatar da sabbin mutane 42 sun kamu da COVID-19 a babban yankin kasar Sin
2020-04-10 11:24:34        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce ta samu rahoton sabbin mutane 42 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19, jiya Alhamis a babban yankin kasar, kuma daga cikinsu 38 shigo da ita suka yi daga ketare.

Har ila yau a jiyan, an sallami mutane 85 daga asibitoci bayan sun warke, inda adadin wadanda ke cikin matsanancin hali ya ragu da 32 zuwa 144.

Ya zuwa jiyan, adadin wadanda aka tabbatar sun shigo da cutar babban yankin kasar daga ketare, ya kai 1,141. Daga cikinsu, an sallami 408 bayan sun warke, akwai kuma 733 dake jinya, inda 34 suke cikin matsanancin hali.

Jimilar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar ya kai 81,907 zuwa jiya, ciki har da 1,116 dake jinya yanzu haka, da 77,455 da suka warke, sai kuma 3,336 da cutar ta kashe. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China