Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na taka rawar gani a kokarin yaki da COVID-19 a duniya
2020-04-10 11:00:28        cri
Jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kokarin yaki da cutar COVID-19 a duniya, bisa manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.

Da yake jawabi yayin wani taron ta bidiyo da babban jami'in MDD kan hakkin bil adama, game da barkewar cutar COVID-19 da tasirinta kan hakkokin bil adama, Chen Xu, ya ce yanzu haka, kasar Sin na kokari wajen taimakawa sama da kasashe da kungiyoyi 130.

Ya ce kasar ta tura jimilar tawagogin jami'an lafiya 13 zuwa kasashe 11, sannan ta yi taron kwararru ta bidiyo har sau 70 da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 150.

Jami'in ya kuma yi kira ga dukkan kasashe su mayar da hankali wajen kiyaye lafiya da rayukan al'umma domin rage tasirin COVID-19 kan 'yancin bil adama.

Ya ce kamata ya yi kasashen duniya su samar da taimako da tallafi ga kasashe masu tasowa wajen tunkarar annobar, yana mai jaddada kira ga kasashen da batun ya shafa, su dage takunkuman da suka sanyawa kasashe masu tasowa domin kaucewa kara jefa al'ummomin kasashen cikin mawuyacin hali.

Dongane da batun nuna wariya da siyasantar da batun lafiyar al'umma, Chen ya ce cuta makiyar dukkanin bil adama ce, kuma ba ta san iyakar kasa ko bambancin kabila ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China