![]() |
|
2020-04-10 11:23:20 cri |
Sakamakon da aka samu ya nuna cewa, yayin da mafi yawan kasashen dake shiyyar suke ci gaba da fuskantar matsaloli iri daban daban sakamakon barkewar annobar COVID-19, hakikanin hasashen karuwar ma'aunin tattalin arzikin (GDP) na kasashen zai fadi warwas musamman a tsakanin manyan kasashen shiyyar 3 mafiya karfin tattalin arziki da suka hada da Najeriya, Angola, da Afrika ta kudu, sakamakon samun koma bayan bunkasuwar tattalin arziki da zuba jari.
Rahoton bankin duniyar ya nuna cewa, akwai yiwuwar matsalar annobar COVID-19 za ta iya shafar abinci a nahiyar Afrika, har adadin hatsin da za a samu zai ragu da kashi 2.6% ko kashi 7%.
Bugu da kari, dangane da irin matakan da ake dauka, kasashe da dama na daukar matakan yaki da annobar COVID-19, inda manyan bankunan kasashen da dama dake shiyyar suke daukar muhimman matakai kamar rage yawan kudin ruwa, da ware kudaden tallafawa tattalin arzikin kasashen, kamar yadda wani masanin tattalin arzikin Afrika dake aiki da bankin duniya Albert Zeufack, ya bayyana.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China