2020-04-08 10:26:00 cri |
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), tana daukar matakan kandagarki na yiwuwar bazuwar annobar COVID-19 a sansanonin 'yan gudun hijira a dukkan yankunan gabashi da manyan tafkunan shiyyoyin Afrika, wadanda suke daga cikin manyan wuraren da 'yan gudun hijira suke samu mafaka a duniya.
A wata sanarwa da ta fitar, hukumar UNHRC ta ce, zama cikin yanayin cunkuso, ba tare da samun ingantaccen ruwa da kayan tsaftar muhalli ba, kuma babu ingantaccen yanayin zaman rayuwa da abinci mai inganci, 'yan gudun hijirar dake yankunan suna cikin yanayin barazanar kamuwa da annobar, ba ma ga su kansu sansanonin 'yan gudun hijirar ba har ma da sauran yankunan birane.
Hukumar UNHCR tana ci gaba da yin aiki tare da ma'aikatun lafiya da hukumomin gwamnati, da hukumar lafiya ta duniya (WHO), domin shigar da 'yan gudun hijirar, da masu neman mafaka da rikici ya raba da gidajensu cikin shirye shiryen da aka tsara gudanarwa a kasashen duniya.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China