Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta harba tauraron dan Adam na karshe da zai yi aiki da tsarin hidimar taswira ta BeiDou
2020-04-06 16:01:36        cri
A watan Mayun dake tafe ne, kasar Sin za ta harba tauraron dan Adam na karshe, wanda zai yi aiki da tsarin hidimar taswira ta BeiDou-3, daga tashar harba kumbuna dake Xichang, na lardin Sichuan, wanda ke kudu maso yammacin kasar.

Sabon tauraron dan Adam din da ake shirin harbawa, zai kasance na 55, a jerin taurarin da suke samar da hidimar taswira ta BeiDou. An kuma tsara isar sa cibiyar Xichang a farkon watan nan, domin harhada shi, da zuba masa mai karfin harba shi samaniya.

Taurarin dan Adam na BeiDou kirar kasar Sin ne, wadanda aka tsara domin samar da hidimomin taswirar duniya, wadanda za su iya samar da fa'idar aiki ga daukacin sassan duniya. Sin ta kuma fara kera tauraron BeiDou-3 ne a shekarar 2009. Kuma harba tauraron na 55, zai kasance matakin karshe na kammalar wannan aiki. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China