Xi: Sin za ta kara taimakon da take baiwa Afirka wajen yaki da COVID-19
2020-04-03 20:17:11 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da taimakawa kasar Namibiya da sauran kasashen Afirka wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19.
Shugaba Xi ya bayyana haka ne Jumma'ar nan, yayin tattaunawa da takwaransa na kasar Namibiya Hage Geingob ta wayar tarho.(Ibrahim)