![]() |
|
2020-04-02 12:09:49 cri |
A ranar 1 ga watan nan na Afirilu, sabuwar masana'antar Tiexi ta kamfanin BMW, wadda daya ce daga manyan ayyukan zuba jarin waje a kasar ta Sin, an fara aikin gina ta a birnin Shenyang na lardin Liaoning.
Bayan zuba jarin da ya kai yuan biliyan 20, kamfanin BMW na Sin, ya zama kamfani mafi girma dake sarrafa hajojin sa, kuma kamfani mafi girma dake gudanar da bincike da samar da ci gaba a wajen helkwatar sa dake kasar Jamus. Kuma tuni karamar hukumar birnin da yake, ta fara aiwatar da matakai daban daban, na tabbatar da nasarar ayyukan kamfanin.
A daya bangaren kuma, an kaddamar da wasu manyan ayyuka 103 a lardin Heilongjiang dake arewacin kasar ta Sin.
Haka zalika, a ranar 31 ga wayan Maris, an kaddamar da ayyukan da suka shafi fannin noma, da raya karkara har 283 a lardin Jiangsu. Domin tabbatar da nasarar wadannan ayyuka, karamar hukumar yankin ta rattaba hannu kan muhimman yarjeniyoyin hadin gwiwa da bankuna, don samar da dandalin samar da kudade, domin cimma nasarar wadannan ayyuka. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China