![]() |
|
2020-04-02 12:03:15 cri |
Yayin wani taron manema labarai ta yanar gizo da ma'aikatar ta gudanar, ta ce za a dauki jerin matakai domin shigar da muhimman sassan masu zuba jari na kasa da kasa a fannin cinikayyar man fetur, da gaggauta samar da sauye sauye, da daga darajar masana'antun sarrafa albarkatun mai da matatun mai, tare da inganta tsarin kasuwannin mai gwargwadon bukata.
Ma'aikatar ta ce tsarin bude kofa a wannan fanni, zai zamo wani jigo na hade manufofin inganta masana'antun mai da iskar gas, kamar sassan cinikayya, da ajiyar albarkatu, da sufuri, da fannin sarrafawa da rarraba hajoji, da fannin hada hadar kudi da haraji.
An kafa yankin cinikayya maras shinge na Zhejiang ne domin samar da damar fitar da tataccen mai, sa'an nan kamfanonin mai musamman ma wadanda ke samar da kayayyakin hadaddun albarkatun mai dake cikin yankin cinikayyar za su fara da fitar da kayayyakinsu zuwa ketare.
Kaza lika za a yi amfani da manufar wajen inganta samar da iskar gas, da hajojin makamashi mai tsafta, da mai mai karancin sinadarin "Sulfur" da kyautata yanayin albarkatun teku, domin kara inganta kiwon lafiya da muhalli mai nagarta. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China