![]() |
|
2020-04-01 20:28:19 cri |
Kwanan baya jaridar New York Times ta wallafa wani rahoto, inda mai tsattsauran ra'ayin nan dan kasar Amurka Stephen K. Bannon ya bayyana cewa, duk da cewa Amurka tana dogara ne kan kasar Sin a bangarori da dama, amma kasashen biyu suna yin kazamin yaki ne a fuskokin ra'ayin jama'a da tattalin arziki, kana ya shafa wa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar kashin kaji cewa, suna kawo wa duniya barazana.
A daidai wannan lokaci mai muhimmanci da kasashen Sin da Amurka ke hada kai a bangaren yaki da annobar COVID-19, wasu Amurkawa marasa kirki da hangen nesa suna yada kwayar cutar siyasa, domin bata sunan kasar Sin, Bannon wanda aka kore shi daga fadar shugaban Amurka yana daya daga cikinsu.
Bai san cewa adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Amurka ya fi na sauran kasashen duniya ba ne? Ko bai san al'ummomin kasar Amurka suna cikin mawuyacin yanayi ba? Ko bai san kasarsa tana bukatar tallafi daga ketare cikin gaggawa ba? Hakika dalilin da ya sa ya nuna kiyayya ga kasar Sin shi ne domin biyan bukatun wasu rukunonin moriyar musamman na Amurka, amma da gaske tsokacinsa yana da hadari matuka, kuma zai iya yin illa ga zaman takewar al'ummar Amurka.
Hakika tsokacin maras hankali na Bannon yana lalata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka, musamman ma kan aikin yaki da annobar COVID-19, dole ne a dakile illar, in ba haka ba, za ta lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka, da ma muradun Amurka baki daya,(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China