![]() |
|
2020-03-31 15:34:40 cri |
Cibiyar yaki da cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar Afirka, ko Africa CDC a takaice, ta ce cutar numfashi ta COVID-19 ta hallaka mutane 146 baki daya a sassan nahiyar daban daban, yayin da kuma ya zuwa ranar Litinin adadin masu dauke da ita kuma ya haura mutum 4,760.
Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, mataimakin daraktan cibiyar ta Africa CDC Ahmed Ogwell, ya ce kawo yanzu cutar ta riga ta shiga kasashen Afirka 46.
Cikin kasashen nahiyar da cutar ta fi kamari dai akwai Afirka ta Kudu mai mutum 1,280, da Masar mai mutane 609, sai Algeria mai mutum 511, yayin da aka tabbatar da harbuwar mutum 479 a kasar Morocco. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China