Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Sin ya ragu zuwa kasa da 3000
2020-03-29 17:19:27        cri
Da yammacin yau Lahadi 29 ga wata, kakakin ma'aikatar lafiyar kasar Sin, Mi Feng, ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 28 ga wata yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin ya ragu zuwa kasa da 3000, kuma an dakile yaduwar cutar a tsakanin jama'a. Rahoton da aka samu na wadanda suka kamu da cutar 693 sun shigo da cutar ne daga kasashen duniya 42, wadanda suka hada har da wasu kasashe 7 da cutar ta fi kamari, inda suka samun kaso 83.4% na yawan wadanda suka kamu da cutar a duniya. Har yanzu akwai yiwuwar samun sabbin wadanda suka kamu da cutar da kuma yada cutar, don haka akwai bukatar ci gaba da daukar matakan yin kandagarkin barazanar yaduwar cutar a tsakanin al'umma da kuma sabbin mutanen dake shigowa da cutar daga ketare, tilas ne a gano su a kan lokaci, domin dakile cutar cikin gaggawa da yin kandagarki yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China