
Tun bayan da aka samu barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Wuhan na Hubei na kasar Sin da sauran sassan kasar, an fuskanci katsewar harkokin yau da kullum a sassa daban daban na kasar Sin, to sai dai a yayin da cutar ke cigaba da yaduwa a sassan duniya kamar wutar daji, a halin yanzu, al'amurra sun fara komawa daidai a yankuna daban daban na kasar Sin tun bayan da gwamnatin kasar ta dauki kwararan matakan dakile cutar ta COVID-19.
Na tuntubi Lawal Tijjani Lawan wani dalibi dan Najeriya dake karatu a jami'ar kiwon lafiya ta birnin Jinzhou dake lardin Liaoning na kasar Sin domin jin halin da ake ciki a yankin, ga karin bayanin da yayi mana.