Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Jimillar mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ta kai 575444 a duniya
2020-03-29 16:32:18        cri

Alkaluman hukumar lafiya ta duniya WHO sun nuna cewa, ya zuwa karfe 18:00 na yamma, agogon tsakiyar Turai a ranar 28 ga watan Maris daidai da karfe 1:00 na safe, agogon Beijing na ranar 29 ga wata, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya ya kai 575,444, yayin da cutar ta hallaka mutane 26654. A halin yanzu akwai mutane sama da 490,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19 a wajen kasar Sin a kasashe da yankunan duniya 201.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China