2020-03-21 15:11:28 cri |
Babban sakataren WHO Tedros Ghebreyesus, ya bayyana a wajen wani taron manema labaru da ya gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland, a jiya cewa, yadda aka daina samun sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a birnin Wuhan na kasar Sin ya karfafa wa mutanen kasashe daban daban gwiwa, da ba su kyakkyawan fatan cewa, duk tsananin da wuyar yanayi, to, akwai damar samun sauki.
Ban da haka kuma, jami'in ya ce, duba da yadda ake fama da matsalar karancin kayayyakin kariya a kasashe daban daban, hukumar WHO za ta samar da tallafi. Yanzu haka hukumar ta tabbatar da cewa, wasu kamfanonin kasar Sin sun riga sun yarda da samar da kayayyakin da ta ke bukata, inda a halin yanzu ake kokarin tabbatar da matakan da za a bi don gudanar da wannan aiki. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China