![]() |
|
2020-03-26 11:18:29 cri |
Babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a jiya Laraba cewa, baya ga daukar matakai na rage cudanyar jama'a da kara nisanta tsakanin mutane, ya kamata kasashen duniya su dauki muhimman matakai a fannoni 6 domin hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ta yadda ba za a dawo da cutar ba, bayan da aka soke dukkanin matakan hana yaduwar cutar.
Bisa sabon rahoton da WHO ta fidda a jiya Laraba, an ce, ban da kasar Sin, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai 332331, yayin da mutane 15153 suka rasa rayukansu. Kana, gaba daya akwai mutane 413467 da aka tabbatar sun kamu da cutar a duk fadin duniya, yayin da mutane 18433 suka mutu, kuma annobar ta shafi kasashe da yankuna har guda 196. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China