![]() |
|
2020-03-24 13:01:44 cri |
Alkaluman da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar na nuna cewa, ya zuwa karfe 6 na yammacin jiya Litinin, agogon tsakiyar Turai, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ya kai 334,981, yawan mamata ya kai 14,510, yawan kasashe da yankuna da aka sanar da bullar cutar ya kai 189.
A jawabin da ya gabatar ta jiya da dare ta kafar talabijin, firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, COVID-19 babban kalubale ne mafi tsanani da kasar take fuskanta a cikin gwamman shekaru, muddin jama'a ba su bi oda ba, to 'yan sanda za su yi amfani da ikonsu, ciki hadda cin su tara da tarwatsa taruruka.
A wannan rana kuma, firaministan kasar Faransa Edouard Philippe ya sanar da cewa, daga yau Talata, za a aiwatar da sabbin matakai. Inda aka tanadi cewa, kowane mutum zai iya fita waje don motsa jiki sau daya a ko wace rana na tsawon sa'a daya, da nisan ba zai gaza kilomita 1 ba, da kuma rufe dukkan kasuwannin sayar da abinci da aka kafa a fili, sannan ba wanda zai iya fito zuwa asibiti sai na bukatar taimakon gaggawa ko likita ya kira shi. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China