Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya ta yi kira da a samar da dakunan gwaji a dukkan sassan kasar
2020-03-20 10:46:19        cri
Shugaban kungiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, Dimie Ogoina, ya ce akwai bukatar gwamnati ta fadada samar da dakunan gwajin cutar COVID-19 a dukkan jihohin kasar dake yammacin Afrika.

Dimie Ogoina, wanda likita ne, ya yi kiran ne cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya a Lagos, yana mai ba da shawarar samar da akalla dakin gwaji guda a kowace shiyya ta kasar.

Ya kara da cewa, za a iya ganin rashin ingantattun matakan shiryawa tunkarar cutar a galibin jihohin kasar, la'akari da rashin kyawun cibiyoyin kebe marasa lafiya da karancin jami'an lafiya da gazawarsu wajen nuna kwarin gwiwar kula da wadanda suka kamu da cutar.

Har ila yau, ya bayyana damuwa game da rashin kayayyakin aiki da ake bukata, kamar na'urorin taimakawa mara lafiya yin numfashi. Likitan ya ce aikin tunkarar cutar a kasar a yanzu, na gudana ne karkashin cibiyar yaki da cututtuka ta kasar da kuma gwamnatin jihar Lagos. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China