Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi da Putin sun tattauna game da karfafa hadin gwiwa domin yaki da COVID-19
2020-03-20 10:36:41        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun zanta ta wayar tarho a daren jiya Alhamis, inda shugaba Xi ya bayyana aniyar kasarsa, ta ci gaba da aiki tukuru tare da sauran kasashen duniya, wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, tare da samar da kariya ga al'ummar duniya a fannin kiwon lafiya.

Shugaba Xi ya ce, bayan barkewar cutar COVID-19 ba zato ba tsammani, kasar Sin ta dukufa wajen tunkarar wannan kalubale, ta kuma yi namijin kokari wajen ganin bayanta. Ya ce baya ga Sinawa, kasar na maida hankali ga kiwon lafiyar al'ummar duniya baki daya.

Daga nan sai ya jinjinawa kwazon da dukkanin sassa masu ruwa da tsaki suka yi, a ayyukan kandagarki da shawo kan cutar a kasar Sin, har aka kai ga dawowar ayyukan masana'antu, da kyautatuwar yanayin zamantakewar al'umma kamar yadda aka saba.

A nasa bangare, shugaba Putin ya ce, jan aikin da kasar Sin ta yi wajen dakile yaduwar wannan annoba a cikin gida, baya ga kawo karshen ta a cikin kasar, ya kuma ba da muhimmiyar gudummawa wajen hana yaduwar ta a sauran kasashen duniya.

Shugaban na Rasha ya ce, kasar sa ta jinjinawa kokarin kasar Sin, duba da irin kyakkyawan misali da ta samar ga sassan kasa da kasa, wajen tallafawa sauran kasashen duniya da wannan annoba ta shafa ba tare da wani bata lokaci ba.

Ya ce abun da kasar Sin ta yi, amsa ce ga wata kasa dake daukar matakan tsokana, da nuna kyama ga Sin, game da ayyukan yaki da cutar COVID-19.

Daga nan sai ya yi fatan ci gaba da aiki kafada da kafada da tsagin Sin, wajen kawo karshen wannan cuta, tare da ci gaba da zurfafa cikakken tsarin hadin gwiwa daga dukkanin fannoni tsakanin kasashen biyu.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China