Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Sin da firaministan Italiya sun tattauna ta wayar tarho
2020-03-17 11:00:08        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya tattauna a jiya da daddare da firaministan kasar Italiya, Giuseppe Conte ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa, sakamakon watanni da dama da aka shafe ana namijin kokari, akwai alama mai armashi a kasar Sin na yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19. Sa'an nan kuma kasar Sin na gaggauta farfado da raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa. Ya ce al'ummar Sin na taka tsan-tsan kamar yadda suka yi a baya, suna kuma ci gaba da kokarin samun cikakkiyar nasarar yaki da annobar, lamarin da zai karfafa gwiwar kasashen duniya wajen yaki da ita.

Shugaban na kasar Sin ya yi nuni da cewa, kasarsa za ta biya bukatun Italiya, kuma za ta kara tura masana kiwon lafiya zuwa Italiyar, tare da ba da tallafin kayayyakin kiwon lafiya.

A nasa bangare, mista Conte ya godewa kasar Sin bisa goyon baya da taimakon da take ba kasarsa a yayin da kasarsa ke cikin mawuyancin hali, lamarin da ya ce, ya sake nuna dankon zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen 2. Ya yi imanin cewa, tabbas zumuncin da ke tsakanin kasashen 2 za ta kara ingantuwa da ganin bayan annobar, (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China