Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Laturoni na kasar Sin ya kaddamar da wata masana'anta a Uganda
2019-11-25 19:36:42        cri
Kamfanin laturoni na kasar Sin mai Engo Holdings Group Limited, ya bude wata masana'antar kera wayoyin salula da kwanfutocin tafi da gidanta da darajarta ta kai dala miliyan biyar a kasar Uganda.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin bude masana'antar a gundumar Mukono dake tsakiyar kasar, Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya yaba wa kasar Sin bisa gudummawar da take ci gaba da bayarwa wajen raya masana'antun kasar.

Ita dai wannan masana'anta, ita ce kashin farko na jarin dala miliyan 15 da kamfanin ya zuba, ana kuma sa ran kamfanin zai samar da guraben ayyukan yi kimanin 500 nan da shekarar 2021. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China