Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban bankin kasar Sin ya samar da rancen kudi RMB biliyan 184 don yaki da COVID-19
2020-03-16 11:27:06        cri
Jiya Lahadi, tsarin hadin kai na kandagarki da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya shirya taron manema labaru, kan yadda ake amfani da manufar kara ba da rancen kudi da ragi, don goyon bayan ayyukan kandagarki da shawo kan annobar, da komawa bakin aiki.

Shugaban sashen kula da manufar kudi na babban bankin kasar Sin, Sun Guofeng ya bayyana cewa, a ranar 31 ga watan Janairu, babban bankin ya shirya rancen kudin musamman na RMB biliyan 300 ga hukumomin kudi don yaki da annobar. Ya zuwa ranar 13 ga watan Maris, bankin ya riga ya samar da irin wannan rance har kudi RMB biliyan 184.

Baya ga haka, jami'in hukumar sa ido kan bankuna da inshora ta kasar Sin ya bayyana cewa, za a dauki matakai hudu, don tabbatar da zaman karkon cinikayyar waje, ciki har da kara wa bankuna karfin gwiwar tattara kudin cinikayya, da inganta da jagoranci hukumomin kudi, wajen kara baiwa sassansu iko a fannin cinikayyar waje, da tsawaita lokacin mayar da kudin da aka aro, da ruwan kudi ga kananan masana'antu masu gamuwa da matsaloli, da kuma inganta mu'amala a tsakanin kananan hukumomin kudi da hukumomin babban bankin kasar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China