Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Magidanta 2,580,000 a jihar Xinjiang sun samu sabbin gidajen dake jure girgizar kasa
2020-01-15 13:31:44        cri
Jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kasance cikin wani zirin da ya ratsa tsakiyar nahiyoyin Turai da Asiya, inda ake yawan samun abkuwar girgizar kasa. Saboda haka ake samun abkuwar girgizar kasa da karfinta ya kai maki 6 ko fiye sau guda a kowace shekara a jihar, yayin da yawan girgizar kasa da karfinta ya kai maki 5 ko fiye da haka da ta abku a jihar ya kan kai sau 5 a shekara guda. Don daidaita wannan matsala, gwamnatin jihar Xinjiang ta fara gina gidaje masu jure girgizar kasa don tsugunar da jama'ar dake zama a kauyuka, tare da cimma nasarori. Alkaluma sun nuna cewa, zuwa karshen watan Disamban shekarar 2019, an raba irin wadannan sabbin gidaje ga magidanta kimanin 2,580,000.

Zhang Yong, shi ne shugaban hukumar tinkarar girgizar kasa ta jihar Xinjiang, wanda ya gaya ma wakilin CRI cewa, a kauyukan da aka gama gina gidaje masu jure girgizar kasa, ko da an samu abkuwar girgizar kasa da karfinta ya kai maki 5, to, ba za ta raunata mutane ba. Har ma a wasu wurare, idan girgizar kasa mai karfin maki 5 ta abku, to, ba sai a aiwatar da shirin tinkarar yanayin gaggawa ba, domin ba za ta yi tasiri kan zaman rayuwar jama'a ba ko kadan, in ji jami'in.

An ce, gwamnatin jihar Xinjiang na kokarin habaka ayyukan gina gidaje masu jure girgizar kasa, don amfanawa dukkan al'ummun jihar a wannan shekara ta 2020 da muke ciki. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China