Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kaso 90 na kamfanonin dake yankunan cinikayya na gwaji 17 sun dawo aiki a kasar Sin
2020-03-13 16:56:46        cri
Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta ce, zuwa jiya ranar Alhamis, ban da lardin Hubei, kimanin kaso 90 na manyan kamfanonin dake yankunan gwaji na cinikayya maras shinge guda 17 a kasar Sin sun farfado da ayyukansu. Kana daga cikin yankuna 55 na kasar, akwai sama da 20 inda kusan dukkan manyan kamfanonin suka sake farfado da ayyukan kere-kerensu.

Ma'aikatar kasuwancin kasar za ta ci gaba da takaita takardar sassan da baki 'yan kasuwa ba za su iya zuba jari ba a yankunan gwaji na cinikayya cikin 'yanci, da kuma gudanar da bincike kan kafa tsarin sa ido kan takardar sassan da baki 'yan kasuwa ba za su iya zuba jari ba na kasuwanci tsakanin iyakokin kasa da kasa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China