2020-03-12 13:10:51 cri |
Ranar Laraba an dawo bakin aikin ginin kafariyar cibiyyar raya kimiyya da fasahar al'adu ta Shanghai Planetarium, kuma ana sa ran cibiyar za ta zama irinta ta farko mafi girma a duniya idan an kammala aikin wanda ake sa ran bude ta a shekarar 2021.
Cibiyar dake sabon yankin Pudong, planetarium tana da girman murabba'in mita 38,164, wanda ya kasance rabin cibiyar raya al'adu ta Louvre dake birnin Paris.
Ma'aikata 22 sun dawo bakin aiki a ranar Laraba, wanda shi ne adadin kashi 15 bisa 100 na yawan ma'aikatan. A yayin da karin ma'aikatan ke dawowa bakin aikin, za'a tabbatar da baiwa rayuwarsu kariya da tsaro, kamar yadda cibiyar adana kayayyakin tarihin ta Shanghai ta sanar.
An dauki tsauraran matakai, tare da gwajin yanayin zafin jiki, da bayanan mutane da sinadaren kashe kwayoyin cuta na hannu da na takalma ga dukkan ma'aikatan da za su shiga yankin da ake gine-ginen cibiyar.
Abubuwan kariya da suka hada da abin rufe baki da hanci, da sinadaren kashe kwayoyin cuta da na gwajin zafin jiki duka an tanade su, a cewar sanarwar.
Cibiyar raya al'adun ta planetarium an tsara ta wadda ta kunshi gine-ginen cibiyoyin bincike da na matasa da kuma wuraren gwaje-gwaje. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China