Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Sin za ta tura tawagar likitoci zuwa Italiya domin dakile cutar COVID-19
2020-03-11 21:03:49        cri
A yau yayin taron ganawa da manema labarai a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokari matuka wajen taimakawa sauran kasashen duniya, domin shawo kan annobar cutar numfashi ta COVID-19, yayin da take gudanar da aikin ganin bayan annobar a cikin kasar.

Geng ya kara da cewa, kawo yanzu kungiyar Red Cross ta kasar Sin, ta riga ta tura tawagogin kwararrun lokitoci zuwa kasar Iran, da kuma kasar Iraki domin samar da taimako gare su wajen dakile annobar cutar COVID-19, har sun samu jinjinawa daga hukumomin da abin ya shafa, da al'ummun kasashen. Kana kasar Sin za ta kara tura tawagar lokitoci zuwa kasar Italiya ba da jimawa ba.

Geng ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe a bangarorin kimiyya da fasaha, kamar su samar da magungunan sha, da maganin rigakafi, da maganin tantance annobar da sauransu, haka kuma tana son samar da dabarun kasar Sin ga sauran kasashe, ta yadda za a ganin bayan annobar tun da wurwuri.(Jamia)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China