Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rikicin kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutane 12 a Habasha
2020-02-28 11:06:46        cri
Wani rikicin kabilanci a jihar Gambella dake yammacin kasar Habasha, ya yi sanadin mutuwar mutane 12.

Da yake zantawa da wata kafar yada labarai, shugaban ofishin tsaro na jihar Gambella, Thomas Tut, ya ce rikicin kabilancin da aka shafe kwanaki ana yi cikin makon da ya gabata, ya samo asali ne daga kisan wani jami'in yankin.

Ya ce kisan jami'in a yankin Nuer na jihar ne ya haifar da mummunan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane 12 da jikkatar wasu 21.

Har ila yau, akwai wasu mutane 7,000 da suka rasa matsugunansu, yayin da aka lallata gidaje sama da 400, tare da sace dabbobin da ba za su gaza 300 ba, yayin rikicin.

A shekarun baya bayan nan, munanan rikice-rikice tsakanin kabilu daban-daban a jihar Gambella, sun yi sanadin rayuka da dama tare da raba dubban mutane da matsugunansu. Galibin rikice rikicen na faruwa ne sanadiyyar neman shugabanci da mallakar filaye.

Habasha na bin tsarin gwamnatin tarayya dake kafa jihohi bisa kabilun jama'a, wanda ya ba da hakkin shugabanci ga kabilu sama da 80 na yawan al'ummar kasar da ya kai sama da miliyan 110.

Sai dai, masu suka na ikirarin tsarin na kara yawan kabilu da raba kan kasa, wanda kan haifar da rikice rikice. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China