Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mujallar The Lancet: Ya dace a koyi fasahohin Sin wajen yakar cutar COVID-19
2020-03-08 16:52:22        cri
A ranar 6 ga wata shahararriyar mujallar ilmin likitanci ta The Lancet ta wallafa wani rahoto, inda aka bayyana cewa, shaidun da aka samu sun nuna cewa, kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi a bangaren kiwon lafiyar jama'a ya riga ya ceto rayukan jama'a wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 sama da dubu goma, a don haka ya dace sauran kasashen duniya su koyi fasahohin da kasar Sin ta samu yayin da suke kokarin dakile annobar cutar.

Rahoton ya ce, kwararrun kasar Sin da hukumar lafiya ta duniya sun fitar da wani rahoto cikin hadin gwiwa bayan binciken da suka yi, inda suka bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakai masu karfi a jere yayin da take kokarin dakile annobar, matakan da suka cimma burin rage adadin mutanen dake kamuwa da cutar da mutanen dake mutuwa a sakamakon kamuwa da cutar. Kana a cikin rahoton, hukumar lafiya ta duniya ta bukaci gwamnatocin kasashen duniya su dauki matakai cikin gaggawa tare da al'ummomin kasashensu, ta yadda za su hana bazuwar kwayar cutar yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China