Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a duniya ban da kasar Sin ya haura dubu 14
2020-03-06 11:02:12        cri

Jiya Alhamis, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO, ta ba da rahoto kan cutar COVID-19 na rana-rana, inda ta ce ya zuwa karfe 10 na safiyar jiya, mutane 14,768 daga kasashe 85 a duniya ban da kasar Sin, suka samu bullar wannan cutar, yayin da wasu 267 suka mutu sakamakon cutar. Adadin ya nuna cewa, sabbin mutanen da suka kamu da cutar a duniya ban da kasar Sin, ya kai 2,098, kari mai yawa idan an kwatanta da Laraba da ta gabata.

Karin kasashe ko yankuna biyar sun gano wannan cutar, ciki hadda Bosnia da Herzegovina, da Gibraltar, da Hungary, da Slovenia, da yankin Palesdinu da aka mamaye.

Rahoton ya kuma nuna cewa, cutar ta yadu a sassan nahiyar Turai, inda kasashe 30 ke dabaibaye cikin wannan annoba. Ya zuwa karfe 10 da rabi na daren jiya bisa agogon Beijing, yawan al'ummar Turai da suka kamu da cutar ya kai 4700, daga cikinsu 3203 'yan Italiya ne, kana yawan mamata ya haura 100, a birane 74 na kasar inda aka gano barkewar cutar. Hakan ya sa ya zama wurin da cutar ta fi kamari a Turai.

Gwamnatin kasar Italiya ta yanke shawarar rufe duk makarantu tun daga ran 5 ga wata, zuwa tsakiyar wannan wata da muke ciki, domin hana kara yaduwar cuta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China