2020-03-04 09:56:50 cri |
Kwararru a hukumar lafiya ta duniya WHO, sun jinjinawa kasar Sin, bisa yadda ta raba kwarewar da ta samu a yakin da take yi da cutar numfashi ta COVID-19 da sauran kasashen duniya.
Da take tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai na rana rana da aka gudanar, jagorar sashen tsara ayyukan gaggawa a fannin kiwon lafiya a WHO Maria van Kerkhove, ta ce ya dace Sin ta ci gaba da raba kwarewarta da sauran sassa a wannan muhimmin aiki, tana mai nuni da tallafin baya bayan nan da Sin din ta baiwa kasar Iran, na kwararru da kayan aiki.
Kerkhove ta ce, wannan kyakkyawan misali ne raba kwarewa tsakanin sassa da dama, wanda kuma ya dace a ci gaba da yin sa tsakanin sauran kasashe, a kuma ci gaba da cudanya domin yaki da cutar.
Jami'ar ta ce, Sin ta yada kwarewarta a fannonin gano kwayar cutar, da dabarun kula da masu dauke da ita, ta tsara asibitocin killace masu dauke da cutar, da ma yadda ake amfani da kayan kariya daga kamuwa da ita. Sauran sun hada da kandagarkin kamuwa da cutar, da kuma dabarun shawo kan ta baki daya.(Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China