Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban bankin Sudan: Amurka ta dage takunkumi kan kamfanonin kasar 157
2020-03-05 10:18:38        cri

Bankin tsakiya na kasar Sudan ya sanar a jiya Laraba cewa, ya samu wasika daga gwamnatin Amurka dake sanar da dage takunkumi kan wasu kamfanonin kasar Sudan kimanin 157.

Badreddine Abdel Rahim Ibrahim, gwamnan babban bankin kasar Sudan ya ce, babban bankin ya samu wasika daga sashen takunkumi na Amurka, inda ya tabbatar da kawo karshen dukkan nau'ikan takunkuman tattalin arzikin da aka sanyawa kasar Sudan. A cewar wasikar, wasu daidaikun mutane da wasu tsirarun kamfanonin ne har yanzu ba'a dage musu takunkumin ba wadanda galibi suke da alaka da rikicin yankin Darfur, har yanzu suna karkashin takunkumin.

Amurka ta kakabawa Sudan takunkumi ne tun a shekarar 1997, inda ta ayyana Sudan cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

A ranar 6 ga watan Oktoban shekarar 2017, Amurka ta yanke shawarar dage takunkumin tattalin arzikin da ta sanyawa kasar Sudan.

Sai dai kuma har yanzu, Amurkar ba ta tsame Sudan daga cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China