2020-02-26 20:42:08 cri |
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, ya zuwa yanzu, shugabannin kasashe 170, da kungiyoyin kasa da kasa 40, sun jajantawa kasar Sin game da aikin tinkarar cutar COVID 19. A cewarsu, Sin tana namijin kokarin aiwatar da matakan yaki da kandagarkin cutar, a sa'i daya kuma, sauran kasashe sun amfana daga dabaru da fasahohin da ta samu.
Zhao ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su yi hadin kai a gabar da ake fuskantar kalubalen lafiya a duniya, don tinkarar matsala tare. Ya ce Sin za ta ci gaba da daukar matakai masu dacewa, domin kandagarki, da yaki da cuta a nan gaba, za kuma ta kara hadin kan da take yi da sassan kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, don tabbatar da raya kyakkyawar makomar Bil Adam ta bai daya. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China