Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha za ta harba tauraron dan Adam da tallafin kasar Sin
2019-11-26 09:22:12        cri
Jakadan kasar Sin a Habasha Tan Jian, ya ce an kammala shirye shirye da suka wajaba, domin harba tauraron dan Adam mallakar Habasha irin sa na farko da kasar ta mallaka da tallafin kasar Sin.

Tan Jian, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin da yake jawabi ga mahalarta wani taro da gwamnatin Habasha, da hadin gwiwar kamfanin sayayya ta yanar gizo Alibaba na kasar Sin suka shirya, da nufin yayata manufar sauya akalar gudanar da ayyuka ta hanyar amfani da fasahohin sadarwa a Habasha.

Jakadan na Sin ya ce, lokaci yayi da a rungumi fasahohin zamani domin cimma nasarorin da ake fata, cikin sauri kuma a kan lokaci. Ya ce batun ya wuce na tafiya sannu sannu, dole ne a yi hanzarin rungumar fasahohin zamani, kamar hada hadar cinikayya ta internet, da fasahar sadarwa, da fasahohin sufurin samaniya.

Rahotanni sun nuna cewa, tauraron dan Adam din na Habasha mai lakabin ETRSS-1, na da nauyin kilogiram 70, kuma za a harba shi ne daga kasar Sin, amma na'urorin sarrafa shi na girke a cibiyar lura da sufurin samaniya dake tsaunin Entoto, dake wajen birnin Addis Ababan kasar ta Habasha. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China