Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalar Masar da sassakar kayan tarihi na Sphinx sun yi ta haska jan wuta domin murnar sabuwar shekarar Sinawa
2020-01-24 14:51:27        cri
Dalar Masar da sassakar kayan tarihi na Sphinx dake Giza, wanda ke kusa da birnin Alkahira, sun yi ta haska jan wuta tare da fitar da sauti, da yammacin jiya Alhamis, a wani bangare na murnar bikin Bazara na kasar Sin, wanda kuma aka sani da sabuwar shekarar gargajiya ta al'ummar Sinawa.

Bikin wanda cibiyar raya al'adun Sinawa dake birnin Alkahira wato CCC, da kamfanin samar da wuta da sauti na Misr, suka shirya, ya samu halartar daruruwan Sinawa tare da jama'ar kasar Masar masu sha'awar al'adun Sinawa.

Shi Yuewen, jami'in kula da al'adu na ofishin jakadancin Sin dake Masar, kuma shugaban cibiyar CCC, ya ce dutsen Dalar ya haska wuta mai ban sha'awa, inda jajayen fitilun Sin suka saje da kayatattun Dalar Masar, wanda ke alamta haduwar kasashen Sin da Masar masu dadadden tarihi.

Ya kuma bayyana cewa, an samu gagarumar nasara a shekarar 2019 da ta gabata, inda aka samu karuwar musayar al'adu da yawon bude ido da kawance tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

A cewar shugaban asusun raya al'adu na ma'aikatar kula da al'adu ta Masar, Fathy Abdel Wahab, hadewar al'adun Sin da Masar na kara karuwar, saboda goyon bayan da ake samu daga shugabannin kasashen biyu. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China