2020-02-14 13:30:41 cri |
Hukumar kiwon lafiya ta lardin Hubei na kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 12 ga wata yawan sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 14840, ciki har da mutane 13332 da aka tantancesu a asibiti bisa alamun kamuwa da cutar da suka nuna. Inda alkaluman sun jawo hankalin jama'a sosai.
Michael Ryan, shugaban kula da ayyukan kiwon lafiya cikin gaggawa na hukumar WHO ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, an samu karuwar yawan sabbin mutanen da aka tabbatar cewa sun kamu da cutar ne saboda an canja hanyar tabbatar da mutanen da suka kamu da cutar. A ganinsa, wannan ya sa likitoci suna iya tantance mutanen da suka kamu da cutar cikin sauri, domin babu bukatar a jira sakamakon binciken kimiyya da aka yi musu, ta hakan za a tabbatar da mutanen da suka kamu da cutar don a yi musu jinya cikin sauri. Haka zalika za a taimakawa mutanen da suka taba yin mu'amala da mutanen da suka kamu da cutar da sauran matakan kiwon lafiya cikin gaggawa. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China