Gwamnatin kasar Sin zata aiwatar da shirin bunkasa ayyukan gona a lokacin bazara kana zata dauki kwararan matakai wadanda zasu bunkasa harkokin kasuwanci da samar da guraben ayyukan yi, wadanda suka kunshi shirin saukakawa ko kuma janye kudaden inshorar wadanda masu samar da guraben ayyuka ke tarawa da kuma dakatar da biyan kudade ga asusun samar da gidaje, a kokarin bunkasa tattalin arzikin kasar.
An dauki wadannan matakai ne a lokacin taron majalisar gudanarwar kasar Sin wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta a ranar Talata. (Bilkisu)