Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana canja sabbin matakan yaki da cutar Corona
2020-02-14 09:54:24        cri

Hukumomi a kasar Sin sun jaddada canja matakan yaki da cutar numfashi da ta bulla a yankunan kasar daban-daban. An dauki wannan mataki ne, yayin taron babban kwamitin kandagarki da hana yaduwar cutar na kwamitin koli na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) da firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta a jiya Alhamis.

Haka kuma taron ya bukaci a kara zage damtse wajen inganta jinyar marasa lafiya da hanzarta bincike don samar da maganin wannan cuta.

Li wanda har ila mamban hukumar siyasa na kwamitin koli na JKS, ya bayyana cewa, abu mafi muhimmanci shi ne matakan kandagarki da hana yaduwar cutar a lardin Hubei, musamman Wuhan, babban birnin lardin. Taron ya kuma umarci birnin na Wuhan da ya hanzarta kwantar da marasa lafiya a asibitoci da ma killace wadanda suka kamu da cutar.

Bugu da kari, taron ya umarci birane a lardin Hubei da cutar ta fi kamari, kamar Xiaogan da Huanggang, da su dauki jerin matakai kamar yadda ake dauka a Wuhan a fannin sanya-ido, da killace wadanda suka kamu da cutar ba da jinya. Wadannan jerin matakai a cewar taron, sun hada da yadda jama'a za su rika dawowa mataki-mataki bayan hutun bikin bazara.

Haka kuma kowa ne lardi, shi zai bulla da matakansa na kandagarki da hana yaduwar cutar bisa yanayin da yake ciki.

Daga karshe taron ya bayyana cewa, kowa ne yanki zai dauki matakan da suka dace da bukatunsa, kuma wajibi ne a gyara duk wasu kura-kurai masu tsauri da ma wadanda ba su dace ba da aka dauka, ba tare da bata lokaci ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China