Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana kokarin inganta ayyukanta na yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19
2020-02-13 17:23:18        cri
Annobar cutar numfashi ta coronavirus da aka fi sani da COVID-19 tana cigaba da haifar da tarin matsaloli da kuma rashin tabbas a kasar Sin da ma duniya baki daya. Nicholas Rosellini, jami'in hukumar MDD dake kasar Sin, ya bayyana ra'ayinsa ga gidan talabijin na CGTN na kasar Sin game da halin da ake ciki da kuma wasu daga irin zarge zargen da ake yi wa gwamnatin kasar Sin kan batun.

CGTN ya tambaye shi ko me zai ce game da yadda ya kalli irin matakan da gwamnatin Sin ke dauka wajen yaki da annobar kawo yanzu?

Rosellini ya ce: Akwai kwararan matakai masu yawan gaske da gwamnatin kasar Sin ta dauka. Kuma abin da kwararrun masana ke cewa shi ne matakan da gwamnatin Sin ke dauka sun taimaka matuka wajen dakile tsananin annobar wadda ta barke a lardin Hubei, alal misali. Kuma hakan na nufin adadin yawan yaduwar annobar yana matukar raguwa, sakamakon daukar matakan. Wannan shi ne fahimta ta.

Abu mafi muhimmanci shi ne musayar bayanai; wato fitar da bayanai. Kuma ina ganin cewa gwamnatin ta taka rawar gani wajen samar da muhimman bayanai a cikin gida da kuma ga duniya baki daya.

Abu mafi muhimmanci shi ne a dauki darrusa daga irin matakan da ake daukar wajen tinkarar matsalar. Kuma ina da tabbacin ko da a matakan kananan hukumomi ma, akwai muhimman darrusa da suka kamata a koya ko da zuwa nan gaba ne game da yadda ake samar da bayanai ba tare da rufa rufa ba da kuma karin musayar bayanan ga al'umma.

Amma idan muka kalli irin matakan da gwamnati ta dauka, tun daga ranar 31 ga watan Disamba, bayan sanar da barkewar wannan sabuwar cuta, za mu iya ganin cewa lallai gwamnati ta mayar da dukkan hankalinta inda ta zuba makudan kudade ga ayyukan kawar da annobar.

CGTN: Wasu suna zargin kasar Sin da rashin gudanar da al'amurra a bayyane a yayin barkewar cutar kuma suna kalubalantar gwamnatin kasar wajen gazawa game da daukar kwararan matakan gaggawa wajen tinkarar batun lafiyar al'umma. Mene ne ra'ayinka?

Rosellini: Idan muka kalli farkon barkewar annobar, ina tunanin za mu iya ganin yadda yanayin cutar yake yaduwa cikin sauri. A kullum akwai sabbin alkaluma dake bayyana sabbin hujjoji da ake fitarwa.

Kuma ina tunanin kowace irin gwamnati, ta kan bukaci dan karamin lokaci domin daukar matakai. Kuma mun ga hakan a matakin farko. Game da matakan da kananan hukumomi ke dauka wajen kai dauki kuwa, ina tunanin ya kamata a yi kyakkyawan nazari game da yadda ya kamata su tafiyar da al'amurra a nan gaba.

Amma ina tunanin abin da muke ta gani tun daga watan Janairu zuwa wannan wata na Fabrairu ya kasance wani muhimmin kokari na tattaro alkaluma da kuma yin musayarsu. Wannan gagarumin aiki ne. Ba karamin aiki bane tafiyar da tsarin ayyukan kula da lafiya a Wuhan. Yanzu annobar ta riga ta yadu zuwa sauran lardunan kasar Sin.

Ayyukan kula da lafiyar ana cigaba da inganatawa kuma ana tafiyar da shi. Amma ina tunanin ya kamata mu lura cewa wannan annobar tana cigaba da yaduwa, kuma yanayin yana sauyawa a kullum. Kuma ina ganin idan muka yi la'akari da yanayin da ake ciki, matakan da ake dauka wajen samar da bayanai game da wannan batu, hakika suna da inganci kamar yadda ake tsammani. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China